(ABNA24.com) A Siriya, sojojin kasar shida ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake kan wani wurin bincike a yankin Deraa dake kusancin kasar.
Wani dan kunar bakin ne kan babur ya tarwatsa kansa a shingen binciken sojojin inda ya kashe shida daga cikinsu tare da raunata wasu da dama, a cewar kungiyar kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriyar dake da cibiya a Birtaniya.
Saidai a nasa bangare kamfanin dilancin labaren kasar Siriya na Sana, ya ce, an samu sojojin da suka jikkata, a harin ta’addancin da aka kaiwa sojojin kasar.
Babu dai wata kungiyar data dauki alhakin kai harin, a wannan yankin da sojojin Siriya suka kwace ikonsa a cikin shekara 2018, ga ‘yan tada kayar baya.
/129
29 Yuli 2019 - 04:02
Lambar labari: 965491
A Siriya, sojojin kasar shida ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake kan wani wurin bincike a yankin Deraa dake kusancin kasar.